
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wani mai shekaru 27 bisa zargin fyaden wata yarinya mai shekaru 5 a al’ummar Pindiga da ke karamar hukumar Akko a jihar.
Kakakin rundunar, ASP Buhari Abdullahi, ya bayyana hakan a ranar Talata a Gombe yayin da ya gabatar da wanda ake zargi da sauran wadanda aka kama.
Abdullahi yace wanda ake zargin ya jawo yarinyar zuwa falon zama inda ya aikata laifin.
A cewar sa, an kai yarinyar asibiti inda likita ya tabbatar da cewa anyi…
>
Leave a Reply