Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta mayar da baburan adaidaita sahun da aka sace guda biyu ga mamallakan su, bayan ta gano su a wata maboyar bata-gari da ke karamar hukumar Danbatta.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Jumu’a.
A cewar sa, an gano baburan ne a ranar 9 ga watan Disamba, sannan aka tabbatar da mamallakan su; Mamman Musa da Sani Isma’il, bayan sun gabatar da cikakkiyar shaidar…
>