Jirgin yakin da zai kaiwa Lakurawa hari ya kauce hanya ya kashe mutane da dama a jihar Sokoto.
An zargi cewa mutane da dama sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani farmakin jirgin yaki da ya yi kuskuren jefa bama-bamai kan wasu al’ummomi biyu a karamar hukumar Silame ta jihar Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe bakwai na safe a ranar Laraba, inda jirgin yakin da aka tura don kai hari kan sansanin ‘yan ta’addan…
>