Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da ayyukan gyare-gyare da za su shafi wutar lantarki a wasu sassan Birnin Tarayya (FCT).
TCN ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Babban Manajan Hulda da Jama’a, Ndidi Mbah, ya fitar a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce injiniyoyin kamfanin za su gudanar da gyare-gyare a tashoshin rarraba wutar lantarki guda biyu daga ranar Asabar zuwa Lahadi.
Sanarwar ta kara da cewa daga karfe 9 na safe zuwa 1 na rana a ranar…
>