Kamfanin Starlink, da ke ba da sabis na intanet ta hanyar tauraron dan adam, ya sanar da karin farashin biyan kuɗin wata-wata a Najeriya.
Sabon farashin zai fara aiki nan take ga sabbin abokan ciniki, yayin da za su fara shafar masu amfani da suka riga suka yi rajista daga ranar 27 ga Janairu, 2025.
A wata wasika da kamfanin ya aike wa abokan hulɗarsa, Starlink ya bayyana cewa karin farashin ya zama wajibi don kyautata hanyar sadarwa da kuma tabbatar da ci gaba da ba da…
>