Masoya Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da dama ne suka yarbe shi bayan dawowarsa daga kasar Egypt a yammacin Alhamis.
Masoya sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero sunyi cikar dango tareda cika tituna domin yin lale marhabun da dawowar Sarkin gida lafiya.
Idan dai za’a Iya tunawa Kimanin makonni biyu Kenan Alhaji Aminu Ado Bayero yabar Kano zuwa kasar Egypt domin ziyarar aiki.
A lokacin ziyarar ne ma Sarkin ya karbi bakuncin kungiyoyi daban daban na Yan Najeriya…
>