Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta kaddamar da Kwamitin Fasaha kan Kula da Jini domin magance matsaloli da inganta ingancin jinin da ake amfani da shi a asibitocin jihar.
A wata sanarwa da mai yadda labarai na ma’aikatar, Ibrahim Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis, 2 ga Janairu, 2025, kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya jagoranci bikin kaddamarwar.
Da yake jawabi yayin kaddamarwar, Dr. Labaran ya bayyana cewa kwamitin an kafa shi ne domin…
>