Kungiyar Darikar Kadiriyya ta kasa reshen jihar Kano, ta kaddamar da bude kafar Radio mai zaman kanta ta farko a nan jihar Kano mai suna “Kadiriyya Radio Nigeria”da nufin yada al’amuran da suka shafi koyarwar addinin Musulunci.
Malam Ibrahim Isah Abdullahi Makwarari, wanda ya jagoranci kaddamar da bude tashar a yau, yace tashar za ta mayar da hankali wajen bayar da gudunmawar koyarwar addinin Musulunci.
Malam Ibrahim Makwarari wanda kuma shi ne shugaban Rabida…
>