Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya aikewa Kiristoci a jihar sakon taya murna yayin da suke bikin Kirsimeti na shekarar 2024.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Yusuf ya bukaci Kiristoci su yi godiya ga Allah da ya ba su damar ganin wannan lokaci.
Ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Dawakin-Tofa, gwamnan ya bukaci Kiristoci da su rungumi mutunta juna da zaman lafiya yayin da suke bukukuwan.
“A yayin da kuke jin daɗin wannan lokaci, ina roƙonku da ku…
>