Gwamnatin Tarayya ta fara jigilar fasinjoji kyauta ta jiragen ƙasa a faɗin Najeriya, da nufin rage wa jama’a wahalar sufuri yayin bukukuwan Kirsimeti.
Muƙaddashin Manajan Daraktan Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC), Ben Iloanusi, ya yi maraba da fasinjojin farko da suka iso tashar jirgin ƙasa ta Kubwa, Abuja, daga Rigasa, Kaduna.
Iloanusi Ya bayyana damuwa kan batun kare lafiyar fasinjoji a wannan rana ta farko, tare da tabbatar da cewa Hukumar na ɗaukar…
>